Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da China Zasu Bari Takunkumin Koriya ta Arewa Sai Ta Yi Watsi Da Mallakar Nukiliya


Shugaban Koriya ta Arewa da shugaban China

Shugaba Trump da Shugaba Xi Jinping sun amince su ci gaba da takunkumin Koriya ta Arewa har zuwa lokacin da ta yi watsi da shirin mallakar makaman nukiliya da ta dukufa a kai.

Fadar gwamnatin Amurka ta White House, ta ce shugaba Donald Trump da takwaran aikinsa, Xi Jingping sun amince cewa za a bar takunkumin da aka kakabawa Korea ta Arewa, “har sai ta kwance damarar kera makamin nukiliya da masu linzami kwatakwata.”

Shugabaninn biyu sun gana ne ta wayar talho da safiyar Jiya Talata, sa’o’i biyu bayan da aka yi wata ganawa tsakanin Xi da Shugaban Korea ta Arewa kim Jong Un, wacce ita ce ganawarsu ta biyu cikin ‘yan makwanni nan.

Kafofin yada labaran gwamnatin China sun ruwaito cewa, Xi da takwaran aikinsa Kim sun gana ne a garin Dalian mai tashar jiragen ruwa, da ke arewa maso gabashin kasar China.

A watan Maris, Kim ya ziyarci Xi, ziyararsa ta farko da ya kai kasar waje a matsayinsa na shugaba Korea ta Arewa, wata alama da ta nuna cewa China na cikin yunkurin da ake yi na kawar da duk wata dama ta mallakar makaman nukiliyan a yankin ruwan Korea.

Xi ya kuma fadawa shugaba Trump cewa, yana goyon bayan wata haduwa da za a yi tsakanin shi Trump da Kim. A watan Mayun nan ake sa ran shugabannin biyu za su hadu ko a farkon watan Yuli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG