Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Hukumar CIA Sun Ci Zarafin Mutane A Afghanistan


Sojojin Amurka a Afghanistan

Binciken da kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ko ICC ta gudanar akan lamuran da suka faru tsakanin shekarar 2003 zuwa 2004 ya nuna alamar cin zarafin wadanda suke tsare a Afghanistan a hannu CIA da sojojin Amurka

Wani bincike da Kotun Laifukka ta Duniya ta gudanar ya nuna cewa mai yiyuwa ne sojan Amurka da Hukumar Leken Asiri ta CIA sun aikata laifukkan yaki ta hanyar anfani da matakan “rashin imani ko na tashin hankali” a yayinda suke yi wa mutanen dake tsare a hannunsu tambayoyi a kasar Afghanistan, galibi a tsakanin shekarar 2003-2004.

A cikin rahoton da take gabatar jiya Litinin ne, wata lauya, Fatou Bensouda tace alamomi na nuna cewa mayakan Taliban, sojan gwamnatin Afghanistan da sojojin Amurka duk sun taka rawa wajen aikata wadanan laifukkan na yaki.

Rahoton yace akwai kuma alamun dake nuna cewa sojan Amurka din sun azabtarda akalla fursunoni 61 tsakanin shekarun 2003 da 2004 a can Afghanistan, yayinda ita kuma CIA ta sa aka gana azaba akan akalla mutane 27 dake tsare a Afghanistan da wasu wuraren asiri dake kasashen Poland, Romania da Lithuania kusan a lokaci guda da na Afghanistan din.

Lauya Bensouda tace nan bada jimawa ba zata yanke shawara akan ko za ta bude cikakken bincike akan wannan al’amari. Kuma koda yake Amurka ba ta cikin wannan kotun ta Manyan Laifukka ta Duniya, ana iya gurfanar da ‘yan kasarta a gaban kotunan kasashen dake cikin kotun, irinsu Afghanistan, don a yi musu shara’a.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG