Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Indiya Sun Rattaba Hannu Kan Wata Muhimmiyar Yarjejeniya


Sakataren tsaron Amurka da Ministan tsaron Indiya

Amurka da Indiya sun rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjajjeniya kan harkokin yau da kullum, wadda ta amince sojojin Amurka da na Indiya su yi amfani da filayen jirgin saman sojin juna wajen gyare-gyare da dakon kaya.

Sakataren tsaron Amurka Ash Carter ya gaya ma manema labarai jiya Litini a hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon cewa Ministan Tsaron Indiya Manohar Parrikar ya rattaba hannu kan yarjajjeniyar a hukumance tunda farko a jiya. Dama Jjagororin tsaron biyu sun jimma amincewa kan yarjajjeniyar a bisa manufa, tun lokacin da su ka hadu a Indiya a watan Afirilu.

Carter ya ce an cimma yarjajjeniyar ce da amincewar bai daya, kuma za ta saukaka harkokin yau da kullum tare da ingantawa.

Jagororin tsaron biyu sun jaddada cewa yarjajjeniyar ba ta amince wata daga cikin kasashen ta kafa sansani a cikin dayar ba, amm kawai don amfani da sansanonin da kayan aikin tare idan bukatar hakan ta taso.

Yayin ziyarar da Parrikar ya kai Pentagon, jagororin tsaron biyu sun tattauna kan ayyana Indiya da Amurka ta yi kwanan nan a matsayin abokiyar tafiya kan batun tsaro.

An bayyana wannan ayyanawarce lokacin da Firaminista Narendra Modi ya ziyarci Washington DC a watan Yuni, kuma Carter ya ce yarjejjeniyar ta amince ma sojojin Amurka su hada kai da na Indiya ta hanyar da ba a yi sai da dadaddun kawayen Amurka na kud-da-kud.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG