Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Yanzu Mata Nada Iko Shiga Can Cikin Masallacin Ali Dargar dake Indiya


Masu zanga-zangar goyon bayan barin mata can cikin masallacin Haji Ali Dargah

A wata gagarumar nasara kuma ga masu kare hakkokin mata, wadanda su ke hankoron ganin an ba su dama sun shiga wuraren ibada a India, wata kotu a birnin Mumbai ta dage dokar da ta hana mata shiga can cikin wani fitacce masallacin nan mai suna Haji Ali Dargah.

Masu hankoron kare hakkokin mata dai, sun yaba da wannan hukuncin kotun, wanda suka kwatanta a matsayin gagarumar nasara da ba wai kawai za ta kawo karshen nunawa mata banbanci da ake yi a wuraren ibada ba, har ma da ikrarin da wasu ke yi na cewa mata ba daidai su ke da maza ba.

Alkalan kotun da su ka yanke wannan hukunci, sun ce haramtawa mata da ake yi shiga masallacin Haji Ali Dargah wanda aka gina shi tun a karni na 15, ya sabawa muhimman hakkokin bil adama, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Alkalan sun kuma ba da umurnin gwamnati ta rika samawa mata cikakken tsaro.

Sai dai har yanzu, kafin a aiwatar da wannan hukunci na barin mata su saka kafarsu a can cikin masallacin, kotun ta ce a dakata har na tsawon makwanni shida, domin a baiwa kwamitin amitattun masallacin damar daukaka kara a kotin koli.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG