Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Kawayenta Zasu Samu Galaba Akan Kungiyar ISIS - Obama


Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama, ya fada jiya Litinin cewa, yana da "kwarin guiwar" rundunar taron dangin da Amurka take yiwa jagoranci zata yi galaba kan kungiyar ISIS, ya kara da cewa, kungiyar tana kara samun koma baya, kuma shugabanninta basu da sauran wurin buya.

"sakonmu garesu mai sauki ne: 'kaine na gaba," inji Mr. Obama a cikin wata sanarwa mai kakkausar lafazi da yayi a helkwatar ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon, bayan da ya gana da majalisar tsaro kan matakai na baya bayan nan a yaki da kungiyar ta ISIS.

Shugaba Obama yayi kokarin ya sake tabbatarwa Amurkawa kan matakan da gwamnatins a take dauka, bayan mummunar harin da mata da mijinta suka kai a garin San Bernadino a jihar California a farkon watan nan, bayan da suka zama masu koyi nda ISIS, da kuma mummunar harin da masu tsatsauran ra'ayi suka kai kan birnin Paris cikin watan Nuwamba.

Amurka inji Mr. Obama, zata ci gaba da yin jogaoranci ga sauran kasashen duniya a yunkurin ganin bayan kungiyar ISIS, mataki da shugaban na Amurka yace yana ci gaba sosai, kuma cikin hanzari.

Mr. Obama bai yi wata sanarwa kan wasu sabbin matakai da gwamnatinsa zata dauka ba, duk da haka yace, sojojin taron dangi zasu ci gaba da farauto da gamawa da shugabannin 'yan ta'adda, ha kalalika ana ci gaba da horasda sojojin Iraqi da samar da musu da kayan aiki harda ma wasu kungiyoyin mayakan sakai a Syria, wadanda suke fafatawa da kungiyar ISIS.

Bugu da kari inji Mr. Obama, Amurka zata ci gaba da aiki na kassara hanyoyin da kungiyar take bi na jawo hankalin mutane su shiga sahunta, da kafofin samun kudadenta da kuma farfagandar da take yi.

XS
SM
MD
LG