Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Koriya ta Kudu sun fara atisayin soja ta ruwa, da yawan sojoji dubu takwas


Lahadin nan Amurka da Koriya ta Kudu suka fara atsai da nufin aikewa koriya ta Arewa da sakon ta shiga tai-tayin ta.

Yau lahadi ce Amurka da Koriya Ta Kudu suka fara wani gagarumin atisayin soji ta ruwa, atisayin da ya sa Koriya Ta Arewa, ta yi barazanar cewa, zai haddasa abin da ta kira “yaki na wajibi ” da zai hada da ta yi amfani makaman Nukiliya.

Atisayin da zai dauki kwana hudu, an yi masa lakabin “Rena kama kaga gayya”,wadda ya hada da sojojin Amurka da na Koriya Ta Kudu su dubu takwas,jiragen yakin ruwa ashirin,ciki har da masu tafiya karkashin ruwa, da jiragen sama na yaki metan, hade da daya daga cikin uwayen jiragen yakin ruwan Amurka mai goyawa da saukar jiragen saman yaki,shi dai wan nan jirgin yana amfani ne da karfin Nukiliya.Sunan sa, USS George Washington.

Jiya Asabar ce majalisar tsaron Koriya TA Arewa ta yi barzanar kaddamar da abin da ta kira “jihadi” kan Amurka da Koriya Ta Kudu,muddin kasashen biyu suka ci gaba da gudanar da wan nan atisayin a kogin nan da ake kira kogin Japan, wani bangare na tekun Pacific dake yammaci.

Atisayin da kuma barazanar ta Koriya Ta Arewa, duk sun biyo bayan nitsar da jirgin yakin Koriya Ta Kudu cikin watan Maris, har ya halaka sojojin kasar 46.

Wani bincike kasa da kasa, ya nuna cewa wani jrigin yaki mai tafiya a karkashin ruwa na Koriya Ta Arewa ne ya har ba nakiyar da ta nutsar da jirgin. Pyongyang dai ta musanta wan nan zargi.

Manyan hafsoshin Amurka da Koriya Ta Kudu duk sun ce atisayin ana yin sa ne da nufin aika sako ga Koriya Ta Arewa a fili cewa ta dai na tsaukana.

XS
SM
MD
LG