Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta sanar da wani Karin tallafin Amurka na dala miliyan dari biyar a Pakistan


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta sanar da wani Karin tallafi na dala miliyan dari biyar a Pakistan, yayinda Amurka ke kokarin neman goyon bayan al’umma a yunkurin yaki da tsaurin ra’ayi.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta sanar da wani Karin tallafi na dala miliyan dari biyar a Pakistan, yayinda Amurka ke kokarin neman goyon bayan jama’a a yunkurin yakar tsaurin ra’ayi a makwabciya Afghanistan. Yayin wani taron manema labarai na hadin guiwa da ministan harkokin kasashen ketare na kasar Pakistan Shah Mehmood Quereshi a Islamabad yau Litinin, Clinton tace inganta ayyukan makamashi da ruwa da lafiya da kuma noma zasu taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Pakistan. Bisa ga cewarta wannan zai kuma taimaka wajen kara dankon dangantaka tsakanin Amurka da Pakistan.

Hillary Clinton and Shah Mahmood Qureshi.
Hillary Clinton and Shah Mahmood Qureshi.

Ayyukan da za a gudanar da tallafin sun hada da dala miliyan dubu da dari biyar da Amurka ta bayar domin tabbatarwa ‘yan kasar Pakistan cewa, ba kawai Amurka tana maida hankali wajen marawa kasar baya ta yaki kungiyoyin Taliban da al-Qaida kadai ba, amma ta kuduri aniyar inganta rayuwar mutanen kasar. Ministan harkokin kasashen ketare na Pakistan Quareshi ya bayyana goyon bayan wannan yunkurin da cewa kulla dangantaka da Amurka ta fuskar ayyukan samar da makamashi da lafiya da ayyukan noma da kuma ilimi na da muhimmancin gaske a Pakistan.

XS
SM
MD
LG