Amurka da kungiyar Taliban sun amince su kafa tawagar kwararru guda biyu domin tantance hanyoyin da za a janye dukkan sojojin Amurka da na NATO daga Afghanistan, da kuma hana 'yan ta'adda amfani da kasar Afghanistan wajen kaiwa Amurka da abokan kawancenta hari.
Babban mai magana da yawun Taliban Mullah Sher Mohammad Abbas Stanikzai ne ya bayyana haka, bayan tattaunawa ta kusan mako guda da aka kammala ranar Asabar a Qatar tare da wakilin musamman na Amurka kan batutuwa da suka shafi Afghanistan, Zalmay Khalilzad.
"A ranar 25 ga Fabrairu, tawagar kwararrun biyu za su tsara su kuma tsaida shawararwari kafin su gabatar a teburin tattaunawar da za ayi a taron da zai gabata a jihar Doha," kamar yadda Stanikzai ya fadi a wata kafar watsa labarai dake goyon bayan kungiyar Taliban. Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya sako faifan bidiyon hirar yau Laraba.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 04, 2023
Amurka Ta Kakkabo Babban Balan-Balan Na Leken Asirin China
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum