Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Mexico Sun Cimma Yarjejeniyar Cinikayya


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Bayan sun kawashe watanni suna muhawara tare da kai da kawowa yanzu Amurka da Mexico sun kulla yarjejeniya akan kasuwanci tsakaninsu ba tare da kasar Canada ba

Yanzu haka, Amurka da Mexico sun cimma yarjejeniyar cinikayya tsakanin su,tare da barin kasar Canada a matsayin saniyar ware, a yunkurin maye gurbin yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen uku, da ake kira NAFTA, kamar yadda shugaba Donald Trump ya bayyana.

Wannan sabuwar yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu za a kira shi yarjejeniyar Amurka da Mexico kamar yadda shugaba Trump ya bayyana.

Yace za mu yi watsi da sunan NAFTA, domin yarjejeniyar ta juma tana cutar da Amurka shekara da shekaru inji Trump.

Trump ya ce wannan wata babbar rana ce ga harkokin kasuwanci, wata babbar rana ce ga kasashen mu, yayinda da shugaban yake magana a gaban manema labarai ta wayar tarho da takwaran aikinsa na Mexico Enrique Pena a ofishin shugaban na Amurka da ake kira "Oval Office.

Shugaban na Mexico ya bayyana fatarsa na sabunta wannan yarjejeniyar. Shiko Trump yana kallon yarjejeniyar wacce ta share shekaru 24 a matsayin matacciya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG