Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Rasha Na Shirin Farfado Da Dantakarsu


Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov sun aminceda tattaunawar yin aiki tare domin farfado da dangantakar dake tsakaninsu, da kuma bude kafofin da za a ke ganawa biyo bayan tattaunawar da aka yi jiya Talata a birnin Sochi.

Ko da yake Pompeo da Lavrov sun tattauna akan matsaloli masu yawa dake tsakaninsu dama na kasashen waje, ciki har da matsalolin da ake fuskanta a Iran da Koriya ta Arewa da Ukraine da Syria da kuma Venezuela, basu dai sami nasarar cimma matsaya akan matsalolin ba.

A taron manema labarai da ministocin biyu suka gudanar bayan tattaunawarsu, Pompeo ya ce Amurka ta shirya gyara dangantakarta da Rasha, amma tana mai sa ran takwararta Rasha za ta dauki abin da muhimmanci.

Wannan shine karon farkoda Pompeo ya taba zuwa Rasha a matsayinsa na sakataren harkokin wajen Amurka. Bayan ganawarsa da Lavrov, jami’an diplomasiyar Amurka sun gana da shugaban kasar Rasha Vladir Putin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG