Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Rasha su daidaita lamura tsakaninsu a yankin Baltics -Admiral Richardson


 Admiral John Richardson na mayakan ruwan Amurka
Admiral John Richardson na mayakan ruwan Amurka

Shugaban sojin ruwan Amurka yace, Amurka da Rasha na bukatar daidaita alakar da ke tsakaninsu a yankin Baltics don kaucewa yiwuwar mummunar arangamar jiragen saman yakin Rasha da jirgin ruwan Amurka.

Admiral John Richardson ya fadawa manema labarai a cibiyar tsaro ta Pentagon a jiya Litinin cewa, haduwar baya bayan nan na Baltics din ya kara haifar da abin da ya kira rashin lissafi, tare da cewa yana fatan wannan abu zai tsaya.

Yace ba ya zaton Rasha na kokarin tsokano wani abu ba ne, to amma yana tunanin wani sako suke son isarwa, na kokarin nuna mana cewa sun san muna nan a yankin na Baltics.

A ranar Juma’a ne jirgin yakin Rasha yayi wani shawagi ta saman jirgin ruwan yakin Amurka da ya tashi ta kan tekun Baltic, makonnin bayan wasu jiragen yakin Rashan sun yi wani shawagin ganganci kusa da jirgin ruwan Amurka a gabar tekeun Kaliningrad.

Rundunar tsaro ta NATO ta karawa sojojinta karfi a gabashin Turai da kuma yanlkin na Baltics, tun bayan da Rasha ta mamaye yankin Crimea ta kasar Ukraine a shekarar 2014.

XS
SM
MD
LG