Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Rasha Sun Amince Za Su Yi Aiki Tare


Rex Tillerson yana jawabi
Rex Tillerson yana jawabi

Ministocin harkokin wajen Amurka da Rasha sun bayyana cewa ba su yarda a ce Koriya ta Arewa ta mallaki makamin nukiliya ba, kuma sun amine da su cig aba da aiki tare domin neman hanyar dakatar da shirin nukiliyar kasar.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, sun amince su ci gaba da aiki tare don neman hanyar dakatar da shirin Nukiliyar zirin Koriya ta hanyar diplomasiyya, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka yau Laraba.

Wata sanarwa daga gwamnatin Amurka ta ce Tillerson da Sergei sun zanta ta wayar tarho jiya Talata don tattauna shirin Nukiliyar Koriya Ta arewa wadda ke iya birkita al’amura a zirin, shirin makaman da Amurka da Rasha duka basu amincce Pyongyang ta mallake su ba.

Kwana daya kafin zantawar, ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta fadi cewa Lavrov ya fadawa takwaran aikinsa na Amurka cewa barazana da cika-baki da Amurka ke yi ta kara zaman fargaba a zirin Koriyar. Rasha ta kuma ce Lavrov ya kira barazanar da Amurka ke yi a matsayin wadda ba ta dace ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG