Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Rasha Sun Cimma Matsaya Kan Kaucewa Karo da Jiragensu a Syria


Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ( a hannun hagu) da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry (a hannun dama)
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ( a hannun hagu) da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry (a hannun dama)

Yarjejeniyar fahimta tsakanin Amurka da Rasha game da ayyukansu a Syria ta fara aiki bayan da suka rattaba mata hannu a jiya Talata.

Kasashen biyu sun yarda zasu tsaya nesa da juna ta wajen amfanin da jiragen samansu don gujewa cin karo da jiragensu.

Kakakin rundunar tsaro ta Pentagon Peter Cook ya ki yarda ya bayyana tazarar da za su bawa jiragen junan a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Amma yace tawagar Amurka ta san takamaimai inda aka shata musu iyakar. Sai dai ana iya cewa duk wani abu da ka iya barazana ko yana iya zama sanadin kaucewa yarjejeniyar za’a kiyayeshi, in ji Mista Cook.

Ya kara da cewa, Rasha ba ta yarda a bayyana manufar yarjejeniyar a fili ba, amma dai ta kunshi kiyayewa tare da kwarewar ayyuka a sama da kuma wasu dabarun hanyoyin sadarwa.

Kakakin ya rufe da cewa, wannan yarjejeniyar ta shafi dukkan jiragen sama ciki har da mararsa matuki, sannan kuma iyakacinta kasar Syria kawai, bata shafi wata kasa ba.

XS
SM
MD
LG