Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Turkiya Suna Sintirin Hadin Gwuiwa Cikin Kasar Syria


Sakataren Harkokin Tsaron Amurka James Mattis

Sintirin hadin gwuiwa da dakarun kasashen Amurka da Turkiya ke yi a birnin Manbj cikin kasar Syria, ma'akatar tsaron Amurka, Penragon ta sanar da hakan

Amurka da kasar Turkiya sun fara sintirin hadin gwuiwa a kusa da birnin Manbj na kasar Syria. Jiya Litinin ma’aikatar tsaro Pentagon ta tabbatarwa Muryar Amurka wannan mataki.

Mai magana da yawun Pentagon Eric Pahon ya fadawa Muryar Amurka jiya Litinin cewa sojojin Amurka suna sintiri a bangare daya yayinda sojojin Turkiya kuma ke sintiri a daya bangaren.

Tunda farko rundunar mayakan Turkiya ta tabbatar da wannan aikin sintiri na hadin gwuiwa ta shafinta na tweeter. A farkon wannan watan Amurka da Turkiya suka yi na’am da taswirar magance rikicin da aka yi watani ana yi akan birnin.

Kasashen biyu sun samu sabanin ra’ayi akan goyon bayan da Amurka ke baiwa kungiyar yan yakin sa kan Kurdawa ta YPK, yan yakin sa kan da Turkiya ta dauka a tamkar kungiyar ‘yan ta’ada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG