Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Turkiya suna yin shawarwari kan yaki da ISIS - John Kerry


John Kerry, sakataren harkokin wajen Amurka
John Kerry, sakataren harkokin wajen Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace Amurka da Trukiya suna shawarwari akan shirye-shiryen fadada hadin kai dangane da yaki da kungiyar ISIS

Jiya Litinin John Kerry ya yi wannan furucin bayan da ya gana da takwaran aikinsa na Turkiya Mevlut Cavusoglu.

John Kerry yace kasashen biyu suna da sha'awar ganin bayan 'yan kungiyar ISIS cikin gaggawa domin maida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Kasar Turkiya kawar kungiyar kawancen tsaron NATO ce. Tana cikin wani bangaren sojojin kawancen taron dangi dake fafatawa da 'yan yakin sa kai na kungiyar ISIS a kasashen Iraqi da Syria.

To saidai duk da haka Amurka da Turkiya suna da sabani akan goyon bayan da Amurka ke baiwa 'yan yakin sa kai na Kurdawa da Turkiya ta ce suna da alaka da kungiyar Kurdistan Workers' Party ko PKK a takaice, wata kungiyar 'yan ta'ada da take yakin samun 'yancin cin gashin kai daga kasar Turkiya

Daruruwan 'yan gudun hijira suke tsarawa kasar Yurkiya saboda gujewa kaungiyar ISIS
Daruruwan 'yan gudun hijira suke tsarawa kasar Yurkiya saboda gujewa kaungiyar ISIS

XS
SM
MD
LG