Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai ta sha alwashin yaki da ta'adanci


Daga hagu zuwa dama ministocin harkokin wajen Belgium da Faransa da Italia
Daga hagu zuwa dama ministocin harkokin wajen Belgium da Faransa da Italia

Biyo bayan hare-haren ta'adanci da aka kai birnin Brussels ministocin harkokin waje da na shari'ar kasashen turai sun yi taron hadin kai domin domin lalubo hanyoyin yakar ta'adanci a nahiyarsu

An yi wani taro biyo bayan harin da aka kai a filin jirgin saman birnin Brussels, inda ministocin shari’a da na harkokin cikin gidan kasashen Tarayyar Turai suna shan alwashin yaki da ta’addanci ta hanyar hadakar bayanan fasinjojin jiragen sama don yakar ta’addanci.

Harin da aka kai kwanakin 3 da suka wuce ya hallaka mutane fiye da 30 ya kuma jikkata sama da 260 a filin jirgin. Ministan harkokin cikin gida na Netherland Ronald Plasterk ya bayyana cewa, kowa ya yarda harin na Brussels ya shafi duk kasashen Turai.

Wannan taron ya wakana a lokacin da hukumomin tsaron Belgium ke ci gaba da fuskantar caccaka game da sakaci da aikinsu na tsaron kasa. Tare da bayyana hujjojin da ke alakanta harin shekaran jiyan da wanda aka kai a watan Nuwambar bara a birnin Paris.

Kwamishinan cibiyar harkokin cikin gidan Turai Dimitris Avramopoulos ma cewa yayi, “wadannan maharani fa girman cikin kasar ne, kuma jami’an tsaro na sane da su. Da ace muna musayar bayanan sirri a tsakanin kasashenmu da ina ganin ba a kai ga haka ba.

XS
SM
MD
LG