Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Majalisa Za Ta Fara Sauraren Bahasi Kan Rahoton Mueller


Shugaban kwamitin da ke kula da fanni shari'a a majalisar wakilan Amurka, Jerrold Nadler, a New York, ranar 29, watan Mayu, 2019.
Shugaban kwamitin da ke kula da fanni shari'a a majalisar wakilan Amurka, Jerrold Nadler, a New York, ranar 29, watan Mayu, 2019.

Nan da wasu ‘yan kwanaki masu zuwa ne, majalisar dokokin Amurka za ta fara sauraren bahasi kan rahoton Robert Mueller dangane da binciken da ya yi kan katsalandin din Rasha a zaben shugaban kasar Amurka a 2016.

Zaman sauraren bahasin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna matsin lamba kan a fara sharar fagen da za ta kai ga tsige shugaba Donald Trump.

Sai dai Mueller wanda ya sauka daga mukamin shugaban kwamitin da ya yi binciken bayan da ya kammala aikinsa, ba zai ba da shaida a gaban kwamitin da ke kula da fannin shari’a ba a majalisar dokokin ta Amurka.

A ranar Litinin mai zuwa kwamitin zai fara aiki kan sauraren bahasin da ya yi wa take da “darasin da za a koya a rahoton Mueller: Yadda shugaban kasa ya yi wa shari’a katsalandan da sauran laifuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG