Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Binciken Musabbabin Mutuwar Sojojinta a Jamhuriyar Nijar


Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis
Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ya tabbatar cewa kasar na binciken musabbabin mutuwar sojojinta hudu a jamhuriyar Nijar da mayakan IS suka yiwa kwantan bauna

Sakataren Tsaron Amurka, Jim Mattis a jiya Alhamis ya ce rundunar sojin kasar na binciken musabbabin mutuwar sojojin Amurkan nan hudu da mayakan jihadi suka kashe a Jamhuriyar Nijar a farkon watan nan.

A ranar 4 ga watan Oktoba mayakan IS suka kai harin kwantan-bauna akan dakarun Amurka hade da na Jamhuriyar Nijar, wadanda su ma an kashe jami’an tsaronsu hudu a harin.

An far ma dakarun Amurkan na musamman ne, jim kadan bayan sun kammala wani taro da shugabannin yankin, a lokacin suna shirin shiga motocinsu, kamar yadda wani jami’in Amurka ya fadawa Muryar Amurka, amma ya nemi da kada a bayyana sunansa, saboda ana kan gudanar da bincike akan harin.

A jiya Alhamis, Darektan Gamayyar rundunar sojojin Amurka, Laftanar Janar Kenneth McKenzie, ya kare sukar da ake wa sojin Amurka kan dalilin da ya sa sai da aka kwashe sa’o’i 48 kafin a gano gawar Saje La Divid Johnson, wanda yana daya daga cikin sojojin Amurka hudu da aka kashe, bayan an jima da kwashe sauran abokanan aikinsa.

“Ba wai mun bar shi a baya ba ne, mun yi ta bincike, har sai da muka gano shi, sannan muka maido da gawarsa gida.” In ji McKenzie, yayin da yake amsa tambayar wani dan jarida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG