Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Bukatar Dala Biliyan 18 Domin Gina Katanga


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Sama da dala biliyan 18 gwamnatin shugaba Donald Trump ke bukata a cikin shekaru 10 domin gina katangar da ta yi iyaka da Amurka da kasar Mexico.

Gwamnatin shugaba Donald Trump ta fada wa majilisar dokokin kasar cewa tana bukatar kudi.

Ta ce ta na bukatar har dala biliyan 18 ne nan da shekaru 10 domin gina katanga a matakin farko tsakanin Amurka da Mexico.

Wadannan kudaden dai za a yi amfani da su wajen gina katangar da take da tsawon kilomita 505.

Gwamnatin ta Trump ta mika wa majilsar a cikin kudaden da take bukata na tafiyar da harkokin hukumar kare bakin iyakonta da kuma na kwastan.

Gaba daya dai gwamnati na bukatar dala biliyan 33 ne wanda za ta kashe domin wannan aikin, ciki har da sama da biliyan 5 na ayyukan fasaha.

Sai kuma biliyan guda na hanyoyi da gyaran su, sai kuma sama da biliyan 8 na kula da jami'an da za su yi wannan aikin.

Ayyukan dai za su hada mutane har 5,000 da za su rika sintiri a wannan bakin iyakar.

Idan dai ba a manta ba shugaba Donald Trump ya yi amfani da wannan batun gina katankar da ta yi iyaka da Amurka da Mexico a daya daga cikin batutuwan da ya bai wa fifiko lokacin yakin neman zaben 2016.

Yanzu haka ma gwamnatin ta Trump ta bukaci Majilisar Dokokin kasar da ta ba ta sama da dala biliyan daya da rabi domin sake katangar da ke da tsawon kilomita 118 a Califonia da Texas.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG