Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Canza Tsarinta Na Raba Rigakafin Cutar COVID-19


Amurka na canza tsarinta na raba rigakafin cutar COVID-19, yanzu kasar ta saki miliyoyin rigakafin da aka ajiye da don zagaye na biyu da za a ba Amurkawa 'yan shekara sama da 65, da kuma wadanda ke fama da wata larurar rashin lafiya.

A lokacin da aka yi hira da shi a wani shiri na gidan talabijin din ABC na safe, sakataren harkokin lafiya na Amurka Alex Azar ya ce tsarin ba da rigakafin a kasar ya maida hankali ne kan bangare guda.

Ya ce amma sabon tsarin ba zai shafi Amurkawan da ke jiran rigakafin kashi na biyu ba.

Yayin da ake samun hauhawar masu kamuwa da cutar COVID-19 a fadin Amurka, shugabannin jihohi da yawa na nuna dari-dari kan daukar karin matakan takaita fita.

XS
SM
MD
LG