Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Fatan Za'a Gudanar da Zaben Nijar cikin Kyakyawan Yanayi da Adalci


Mr.Morou Amadou ministan shari'ar kasar Nijar
Mr.Morou Amadou ministan shari'ar kasar Nijar

A wata sanarwar da ta fitar a jiya Talata Kasar Amurka ta bayyana kyaukyawar niyar taimakawa jamhuriyar Nijer danganin an gudanar da zabubukan badi cikin kyaukyawan yanayi nakwanciyar hankali da fahimtar juna domin tabbatar da demokradiya mai dorewa.

Shekaru biyar kenan bayan da Nijer din ta sake rungumar wannan tafarki.

Sanarwar wace aka rarabawa ‘yan jarida ta fara da cewa kasar Amurka na goyon bayan tafarkin demokradiyar dake gudana cikin yanayi na kwanciyar hankali da adalci domin hakan ne kawai ke bada damar a shirya zabe na gaskiya mai ‘yan takara da yawa.

Saboda haka ne gwamnatin Amurkata yanke shawarar bada gudunmowa a shirye shiryen zabubukan da Nijer ta sa gaba. Alal misali ofishin jakadancin Amurka a Nijer da hukumar USAID sun dauki alkawalinkebe dala miliyan kusan 2 da rabidomin shirye shiryen zabe a kasar .

Daga cikin aiyukan da za’a yi ta hanyar anfani da wadanan kudade akwai maganar jan hankalin jam’iyun siyasa su gane mahimmancin maida hankali akan batutuwan da suka shafi bukatun talakawan kasar Nijer sannan a wani shirin hadin gwuiwa hukumar USAID da kungiyar WANEP zasu dage a aiyukan riga kafin kaucewa tashe tashen hankula a lokutan zabe ta hanyarsamarda bayanan abubuwan dake faruwa a yankunan karkara akai akai domin tabbatar da cewa al’amura na tafiya cikin ruwan sanyi a yayin zabubukan na badi.

Sanarwar ta ofishin jakadancin Amurka a Yamai ta kara da cewa Amurka ta dauki dawainiyar wani ayarin aiyukan waye kan matasa ta hanyar kungiyar YALI domin fadakar da al’ummar Nijer domin zaburarda matasa su shiga da dimbin yawa a dama da su a dukkan zabubukan da za’a gudanar a shekarar 2016.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG