Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Sa Ido Kan Atisayin Da Sojojin Iran Ke Yi A Tekun Persia


John Richardson babban hafsan sojojin ruwan Amurka
John Richardson babban hafsan sojojin ruwan Amurka

A cewar Admiral John Richardson Amurka na sa ido akan atisayin da sojojin ruwan Iran ke yi a tekun Persia tare da cewa zasu tabbatar sun kare walwalar zirga zirgan jiragen ruwa a hanyoyin yankin tekun

Shugaban rundunar sojin ruwan Amurka, Admiral John Richardson, ya ce suna ci gaba da sa ido, kan atisayen da sojin ruwan Iran ke yi a Tekun Persia, kuma za su tabbatar da cewa ba a samu cikas ba wajen samun walwalar zirga-zirgar jiragen ruwa a muhimman hanyoyin da ke wannan yankin tekun, wanda Iran ta ke barazanar za ta rufe.

Rundunar sojin ruwan Amurka, kan kare ka’idojin zirga-zirga akan tekun, wadanda suke ba da damar ratsawa ta wannan mashigi.

Yankin na Tekun Persia, wanda ke gabar gabashin tekun a yankin mashigin Hormuz, na daya daga cikin muhimman hanyoyin fitar da kayayyaki zuwa kasashe a duniya.

Kwanan nan, rundunar sojin juyin-juya halin kasar ta Iran ta IRGC, ta yi barazanar rufe wannan mashigi.

Wani jami’in Amurka ya fadawa Muryar Amurka cewa, manya-manyan jiragen ruwan Iran sun hallara a wannan yanki domin gudanar da atisayen soji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG