Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Gina Ganuwa Kan Iyakar Ta Da Mexico


 Iyakar Amurka Da Mexico
Iyakar Amurka Da Mexico

Shugaban Amurka Donald Trump yana shirin bada umarnin gina ganuwa kan iyakar Mexico, da kuma daukar matakin wucin gadi na kayyade wadanda ake ba izinin shiga kasar, bisa ga wadansu jami’an gwamnati da dama da kuma kwararru a fannin shige da fice.

Ana kyautata zaton yau laraba zai sa hannu a umarnin da ya shafi harkokin shige da fice na farko lokacin da ya ziyarci ma’aikatar harkokin tsaron cikin gida.

Wannan na daga cikin alkawuran yakin neman zabe da ya yi da nufin kara daukar matakan tsaron kasa.

Trump yana so a gina ganuwa a duk fadin iyakar Amurka da Mexico. Yanzu haka akwai shinge a wadansu bangarorin kan iyakar ne kawai. Ya sha yin alkawarin cewa, kasar Mexico ce zata biya kudin gina ganuwar, ya kuma ce, da farko majalisa zata ba gwamnati izinin biyan kudin ginin daga baya gwamnatin kasar Mexico ta biya.

Kasar Mexico dai ta sha bayyana cewa, ba zata biya kudin gina ganuwa ba. Ana kyautata zaton shugaban kasar Enrique Pena Nieto zai ziyarci fadar White House mako mai zuwa.

Wadanda suka fahimci umarnin da ya shafi shige da fice sun ce Trump yana tunanin dakatar da shigar ‘yan gudun hijira na tsawon watanni hudu, da kuma hana ‘yan kasashen Iran da Iraq da Syria da Somalia da Sudan da kuma Yemen shiga Amurka na tsawon kwanaki talatin. An hakikanta cewa, umarnin ba zai shafi tsiraru da ake kuntatawa a kasashensu ba sabili da banbancin addininsu.

XS
SM
MD
LG