Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Kara Haraji Kan Wasu Kayayyakin China


Gwamnatin Shugaba Donald Trump na shirin sanya karin harajin kudaden kimanin dala biliyan 200 kan wasu kayayyakin China, abin da ya kara ruruta rikicin cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu da suka fi karfin tattalin arziki a duniya.

A yammacin jiya Talata, wakilin Amurka kan harkokin cinikayya, Robert Lighthizer, ya fidda jerin kayayyakin China da ta yiwu a kara musu haraji, ciki har da jakar hannu ta mata, akwatunan matafiya, da tayayoyin mota da sinadirai, har da ma kifi.

kudurin karin harajin na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da gwamnatin Trump ta sanya haraji na kashi 25 cikin 100 kan kayayayakin China fiye da 800 da darajarsu ta kai kudi dala biliyan 34, saboda abin da Amurka ta kira “rashin adalci a cinikayyar China” da kuma satar fasaha. Ita ma China ta maida murtini ta hanyar kara haraji kan kayayayakin Amurka na daidai addadin karin da aka yi mata.

Lighthizer, a sanarwar karin harajin ya fadi cewa, maimakon China ta duba damuwarmu ta maganceta, sai ta fara maida martini kan Amurka, babu dalilin daukar wanna matakin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG