Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka na shirye-shiryen karramawa da yiwa marigayi Sanata John MacCain jana'iza


Marigayi Sanata John McCain
Marigayi Sanata John McCain

Cikin wannan makon za'a fara karrama marigayi Sanata John McCain tun daga jiharsa ta Arizona har zuwa Washington DC babban birnin Amurka inda ya kasance dan majalisar dattawa har ya zuwa lokacin mutuwarsa

Za’a karrama Senatar John McCain wanda ya mutu shekaranjiya Asabar bayan ya yi fama da sankaran kwakwalwa. Za’a yi karramawar a jihar Arizona da nan birnin Washington DC.

Da farko za’a ajiye gawar Senata McCain a Phoenix baban birnin jihar Arizona, inda za’a yi bikin tunawa da shi jibi Laraba idan Allah ya kaimu, ranar da zai cika shekaru tamanin da biyu da haihuwa da yana da rai. Ana sa ran mutane za su yi layin kalon gawarsa domin yi masa ban kwana

A ranar Alhamis za’a yi adu’o’in tunawa da shi a cocin darikar Baptist a birnin Phoenix ta arewa. A ranar juma’a idan Allah ya kaimu za’a ajiye gawar senata Mccain a cikin ginin Majalisar dokokin Amurka, inda za’a gayyaci jama’a su kali gawar. Senata Mccain zai zama senata na goma sha uku da za’a ajiye gawarsa a cikin ginin Majalisar dokoki a irin girmamawar da ake yiwa Amurkawa da suka yi fice.

Za’yi adu’o’in tunawa dashi a baban cocin birnin Washington DC a ranar Asabar. Ana sa ran tsoffin shugabani irin su Barack Obama da George W. Bush za su yi jawabai a zaman adu’o’in da za’a yi a nan Washington DC.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG