Amurka ta bayyana wani sabon salonta na fuskantar harkokin Afirka a jiya Alhamis wanda aka tsara da zummar kare muradun Amurka, da kuma kalubalantar yinkurin kasashen China da Rasha na kulla huldar tattalin arziki, da siyasa da kuma tsaro a fadin nahiyar ta Afirka.
A wata rubutacciyar takarda, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, John Bolton, ya bayyana manufofin, wadanda aka kasabta su zuwa sassa uku, wadanda akasari, cigaba ne da matakan Amurka ta fuskar soji, da cinakayya da kuma tallafi a nahiyar ta Afirka.
Abin da ke sabo kawai shi ne, batun dukufa kan shirye-shiryen da za su iya yada muradun Amurka muraran, da kuma himma wajen hana China da Rasha yin kane-kane a Afirka.
Wannan mataki ne da ya ba da fifiko kan muradan Amurka da kuma huldar bangarorin biyu, a cewar Jennifer Cooker, Shugabar Tsangayar Nazarin Harkokin Afirka ta Jami'ar George Washington, a hirarta da Muryar Amurka.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 30, 2023
Kamala Harris Ta Gana Da Mata ‘Yan Kasuwa Na Kasar Ghana
-
Maris 29, 2023
Zimbabwe Na Duba Yiwuwar Soke Hukuncin Kisa
-
Maris 29, 2023
Rundunar Sojojin Kasar Zimbabwe Ta Nemi Tallafin Najeriya.
Facebook Forum