Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Tattaunawa Da Kawayenta Kan Zabin Amfani Da Karfin Soji A Libiya


Wani Sanfurin Jirgin Yakin Amurka.

Amurka ta ce ta na tattaunawa da kawayenta game da zabin daukan matakan soji kan Shugaban Libiya Moammar Gaddafi mai kokarin murkushe dakarun da ke kokarin kawo karshen shugabancinsa na kama karya mai tsawon shekaru 42

Amurka ta ce ta na tattaunawa da kawayenta game da zabin daukan matakan soji kan Shugaban Libiya Moammar Gaddafi mai kokarin murkushe dakarun da ke kokarin kawo karshen shugabancinsa na kama karya mai tsawon shekaru 42.

Jami’an gwamnatin Amurka sun fadi jiya Litini cewa ana auna dukkannin zabi, ciki har da hana jiragen saman Libiya shawagi a wasu sassan kasar don hana jiragen yakin Gaddafi cigaba da kai hari kan ‘yan tawayen da ke iko da gabashin kasar da ma wasu sassan yammacin kasar. Firayim Ministan Burtaniya David Cameron y ace Ingila ma na duba batun hana jiragen Libiya shawagi a wasu wuraren kasar.

Kwamandojin sojojin Amurka sun ce suna matsawa da kayan yakin ruwa da na sama zuwa Libiya don baiwa gwamnatin Obama zabin ayyukan jinkai ko kuma wasu ayyukan.

Ma’aikatar Harkokin wajen Amurka t ace Amurka na tattaunawa da shugabannin ‘yan adawar Libiya a ‘yan kwanakin nan don ta san bukatunsu da kuma abun da ke masu barazana. To amman Jakadiayr Amurka a Majalsiar Dinkin Duniya t ace lokaci bai yi bad a zxa a fara tattaunawa kan agajin soji ga ‘yan adawa a sa’ilinda bangarorin ‘yan adawar ke kokarin hada kawunansu.

Amurka na kuma takurawa gwamnatin Gaddafi ta fuskar kudi, inda ta haramta wa iyalansa amfani dad ala biliyan 30 na dukiyar das u ka adana a Amurka bayan takunkumin da aka kakaba masu a makon jiya.

XS
SM
MD
LG