Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Tuhumar Rasha Da Yin Katsalandan A Zaben Shugaban Kasa Na 2016


Shugaban Rasha Vladimir Putin

Dambarwar siyasar Amurka ta dau wani sabon salo bayan da Amurka ta gabatar da dalla-dallar zargin da ta ke ma Rasha na yin katsalandan a zaben 2016.

Mai bincike na musamman kan katsalandan din da ake zargin Rasha da yi a zaben Amurka na 2016, jiya Jumma’a ya tuhumi wani kamfanin Rasha wanda ya yi shigar burtu ya na aika-aikarsa ta kafar sada zumunta, da kuma ma’aikatan kamfanin su 12 da mai samar da kudin tafi da kamfanin, a tuhuma ta farko da aka yi ma ‘yan Rasha da ake zargi da katsalandan a zaben na Amurka.

Tuhumar, wadda wani gangun masu taya alkali yanke hukunci ya yi a nan Washington DC, ta hada da zargin cewa kamfanin, mai suna Cibiyar Bincike Ta Yanar Internet, wanda ke birnin St. Petersburg, wanda kuma ke da alaka da Fadar Shugaban Rasha ta Kremlin, ya kaddamar da wani shiri na goyon bayan Shugaba Donald Trump a zaben 2016.

Masu gabatar da kara sun kuma tuhumi mai samar da kudin tafi da kamfanin, wani dan kasuwa a Rasha mai suna Yevgeny Prigozhin da wasu kamfanonin kuma biyu da ke karkashinsa.

Mataimakin Attoni-Janar din Amurka Rod Rosenstein ya ce ‘yan Rasha sun hada baki wajen yinkurin haddasa rashin jituwa a Amurka da kuma cusa shakku a zukatan mutane game da sahihancin dimokaradiyya.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG