Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Wofinta Tuhumarta Da Shish-shigi A Zaben Amurka


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Babban mai ba Amurka shawarwari kan harkokin tsaro, Janar H. R. McMaster yace reshen ya juya da mujiya a amfani da hanyar sadarwar internet da Rasha tayi da nufin yiwa Amurka shishshigi.

Mosco ta bayyana cewa, zargin Rashawa 13 da kuma wadansu kamfanonin Rasha uku da katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na shekara ta dubu biyu da goma sha shida shirme ne kawai.

Da yake jawabi a wajen wani taron harkokin tsaro a Munich, kasar Jamus, inda shugabannin kasashen duniya da dama suka hallara, ministan harkokin kasashen ketare na kasar Rasha Sergey Lavrov ya kalulabanci hujjojin ma'aikatar shari'a da kuma kwamitin bincike na musamman da Robert Mueller ke jagoranta.

"Yace bani da ta cewa ko kadan, domin mutum zai iya wallafa abinda ya ga dama. Munga yadda zargi da maganganu suke bazuwa. Sai mun ga shaidu na zahiri, idan ba haka ba duk shirme ne, kuyi mani hakuri domin amfani da kalmar da bata dace da diplmasiya ba"

Binciken na kwamitin Mueller ya yi karin haske kan yunkurin Rasha na yin katsalandan a harkokin siyasar Amurka ta hanyar sadarwar internet. Bisa ga binciken, Rasha tayi amfani da wadannan hanyoyin farfadangar, wajen hada baki a aikata laifi da leken asiri, da nufin yin katsalandan a yakin neman zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida ta wajen goyon bayan Donald Trump ya bakanta abokiyar takararsa Hillary Clinton.

Tuhumar Rashawan ta janyo saiko a taron shugabannin siyasa da na ayyukan soji na kwana uku da ake gudanarwa a Munich.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG