Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Obama Ya Goyi Bayan Biden


Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana goyon bayansa ga tsohon mataimakinsa, Joe Biden, mai takarar mukamin shugaban kasa.

Obama ya kwatanta Biden a matsayin "zabi mafi cancanta" dai zai maye gurbin Shugaba Donald Trump, a zaben da za a yi a watan Nuwamba.

“Makomar kasarmu ta dogara kan wannan zaben,” a cewar Obama.

Amma ya kara da cewa, ba fa abu ne mai sauki ba, kayar da Trump, wanda yayi galabar ba-zata a 2016 kan tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton.

Obama ya yi kira ga Amurkawa da su ci gaba da, abin da ya kira, “yin imanin cewa ta yi wu duniya ta kyautatu” ta wajen bayar da goyon bayansu ga kwamitin yakin neman zaben Biden.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG