Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Dakatar Da Tallafin Da Take Ba Rundunar Sojin Somaliya


 FILE - Somali police march during a ceremony in Mogadishu, Dec. 20, 2008. The ceremony marked 65 years since the academy was established in 1943.
FILE - Somali police march during a ceremony in Mogadishu, Dec. 20, 2008. The ceremony marked 65 years since the academy was established in 1943.

Kasa yin bayani akan kudaden da Amurka ke bawa sojoji a kasar Somaliya ya tilasta wa Amrkan janye taimakon da takeyi domin rashin tabbacin inda ake amfani da tallafin.

Jiya Alhamis jami’an Amurka sun tabbatarwa da muryar Amurka cewa za a dakatar da irin agajhin da ake ba rundunar sojojin Somaliya a bisa damuwa kan zarmiya da cin hanci.

Dakatarwar ta biyo bayan gazawar da sojojin na Somali sukayi wajen bada bayanai akan tallafin da akayi musu na abinci, makamai da ma man fetur.

Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka yace za a dakatar da bayar da agajin na wani lokaci ne domin a tabbatar da cewa ana amfani da tallafin da Amurka ke bayarwa yadda ya kamata ta kuma hanyar da ake bukata.

Amman Jami’an tsaron Somali wadanda a yanzu suke yaki da Yan ta’addar Al shabbab kuma suna samun horo daga Amurka ko wadansu kasashen, zasu ci gaba da samun tallafin da ya dace.

Jami’ar ta kara da cewa gwamnatin Somaliya ta amince da fito da wani tsari na bin diddigi wanda zai iya biyan muradun bin kwakwaf na Amurka domin sauran bangarorin na Somali su ci gaba da samun tallafi daga Amurkar.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG