Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Muka Kai Hari Syria - Amurka


Yadda sararin samaniyar birnin damascus ya
yi haske a lokacin da Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai hari. Ranar 14, Afrilu 2018.
Yadda sararin samaniyar birnin damascus ya yi haske a lokacin da Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai hari. Ranar 14, Afrilu 2018.

Yayin da ake ci gaba da tsokaci kan hare-haren da Amurka ta jagoranta a Syria, Amurkan ta kare kanta dangane da dalilan da suka sa ta kai harin.

“A shekarar 2013, gwamnatin shugaba Putin ta yi wa Duniya alkawarin cewa za a lalata makaman Syria masu guba, amma harin da Assad ya kai a kwanan nan da kuma harin martani da muka kai, sun samo asali ne saboda gazawar da Rasha ta yi wajen cika alkwarinta." inji shugaba Trump

Ya kara da cewa "ya zama dole Rasha ta yi karatun-ta-nutsu, kan ko za ta ci gaba da bin wannan tafarki, ko kuma za ta bi sahun kasahen Duniya wayayyu domin tabbatar da zaman Lafiya.”

Shugaban Amurka Donald Trump, ya yabi Faransa da Birtaniya, saboda goyon bayan da suka bashi wajen kai hare-haren sama akan Syria, a wani mataki na mayar da martani ga shugaba Bashar Al –Assad da ake zargi da yin amfani da makamai masu guba a karshen makon da ya gabata a kusa da Damasacus.

“Na gode Faransa da Birtaniya, saboda hikima da karfin sojin da suka nuna, aiki ya kammalu tsaf!” Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Jiragen saman yakin kasashen Yammaci da na ruwa, sun yi lugudan wuta akan wasu cibiyoyin bincike na kimiyya a kasar ta Syria, a wani matakin hadin kai da kasashen suka nunawa juna, wanda ake tunanin zai dore.

Sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis, ya fada jiya Juma’a a wani jawabi da ya a Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon cewa, wadannan hare-hare sako ne aka ake wa da shugaba Assad.

“A wannan karon, mu da kawayenmu, mun kai hare-hare masu muni, bakin dayanmu, mun aike da sako karara ga shugaba Assad tare da kwamandodinsa masu kisan gilla, saboda haka, kada su kuskura su sake kai wani hari a nan gaba.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG