Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Aika Da Jiragen Yaki Tekun Kusurwar Koriya


Jirgin Ruwan dake dauke da jiragen yaki
Jirgin Ruwan dake dauke da jiragen yaki

Wasu masana sun fara bayyana damuwar cewa aika giggan jiragen ruwa na yaki da Amurka tayi zuwa kusa da Korea ta Arewa, Shugaba Donald Trump na nuna alamar kamar zai maida hankali akan bukatun Amurka fiye da kawayenta na kasashen dake wannan yanki.


Barazanar anfani da karfin soja akan Korea ta Arewa ya dada samun karin muhimmanci ne biyo bayan farmakin da Amurka ta kaiwa Syria sakamakon amfani da makamai masu guba da Syriar ta yi akan mutanenta.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson yace farmakin da sojojin Amurka suka kai akan Syria kashedi ne ga sauran kasashe, ciki har da Korea ta Arewa da ka iya huskantar irin wannan martani, idan suka yi wani abinda ake gani a matsayin barazana.

Sojojin ruwa na yiwa jiragen dake kan jirgin ruwa lodin kayan yaki
Sojojin ruwa na yiwa jiragen dake kan jirgin ruwa lodin kayan yaki


Wani dan kasar ta Korea ta Arewa mai sharhi a kan harkokin kasar, Ahn Chan-il wanda yake tare da cibiyar nazarin Korea ta Arewa ta duniya, yace yana kyautata zaton shugaba Kim Jong Un yana tsoron ganin irin wannan martani.


Rundunar sojan ruwa ta Amurka a yankin Pacific tace ta kudurta aika wadannan jiragen ruwan yaki na rukunin Carl Vinson, mai dauke da jiragen sama tare da wasu jiragen ruwa ‘yan rakiya, zuwa yankin na Koriya ne a matsayin wani matakin rigakafi , a dalilin abinda ta kira “halin rashin tunani da izgilancin da Pyongyang hade da yawan gwaje-gwajen makaman nukiliya da masu libzame da take yawan yi.


Kakakin ma’aikatar tsaron Korea ta Kudu, Moon Sang-kyun ya fada a yau Litinin cewar, girke wadanan jiragen ruwan yakin na Amurka wani matakin kariya ne aka dauka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG