Accessibility links

Amurka ta bullo da wani shirin taimaka wa Afirka

  • Ibrahim Garba

Shugaba Barack Obama na Amurka

Amurka ta yi shelar bullo da wani shiri don amfanar yankin Afirka da ke Kudu da Sahara

Amurka ta yi shelar bullo da wani shiri don amfanar yankin Afirka da ke Kudu da Sahara, ta wajen inganta dimokaradiya da tattalin arziki da tsaro da kuma harkokin cinakayya a yankin.

Wani bayanin Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House da aka fitar jiya Alhamis, ya bayyana cewa matakin da shirin zai dauka game da matsalolin Afirka shi ne na rigakafinsu tun kafin su auku da kuma tinkararsu tun kafin su iso, kuma za a dau matakan ne tare.

Manufar shirin shi ne a bunkasa dimokaradiyya a Afirka, ta wajen karfafa magudanan iko don a sami shugabanci na gaskiya da rikon amana da zai jaddada hakkin dan adam da kuma bin doka da oda. Shirin zai kuma kalubalanci shugabannin da take-takensu ke illa ga sahihancin tsarin dimokaradiyya.

An bayyana sabon tsarin ne a yayin da jami’an Amurka ke karbar bakuncin taro kan Kudurin Cigaban Afirka da samun sukuninta, GOA a takaice na 2000. Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta ce dokar ta haifar da sabbin ayyukan yi da wasu sabbin fannoni a sha’anin tattalin arziki Afirka.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG