Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: Hukumar FBI ta Cafke 'Yan Ta'ada da Dama


Shugaban Amurka Barack Obama

Gabanin bikin tunawa da ranar da Amurka ta samu 'yancin kai hukumar FBI ta cafke wasu da take zargin 'yan ta'ada ne da suka shirya kai hare hare lokacin bikin.

Shugaban hukumar binciken manyan laifukka ta Amurka ta FBI, James Comey ya fada a jiya Alhamis cewa jami’an hukumar sun tarwatsa shirye-shirye da dama na makarkashiya kawo hare-haren ta’addanci a lokacin shagulgullan ranar bukin samun ‘yancin kai a Amurka.

Alokacin da yake magana da manema labarai Comey yace yayi imanin aikin da suka yi ya ruguza shirin kashe mutane da dama da aka kulla, mai alaka da ranar bikin samun ‘yan cin kai na 4 ga watan Yuli.

Yace an kame sama da mutane 10, amma bai bayar da wani bayani kan abunda mutane ke shirin aikatawa ba, ko inda suke shirin kai harin.

Daman dai Ma’aikatar ta FBI da ma’aikatar harkokin wajen Amurka sun fitar da gargadi kan cewa za’a iya kai hari a ranar 4 ga watan Yuli a Amurka, lokacin da miliyoyin Amurkawa ke hidimomin holewa da dama da suka hadada gashe-gashen nama da wasa da wuta.

Comey yace kungiyar IS tayi ta karfafawa magoya bayanta cewa su kai irin wadanan hare-haren akan Amurka, hakan ne yasa aka kama wadansu mutane da ke magana da kungiyar ta wasu hanyoyin sadarwa.

Yace jami’an FBI sun fuskanci kalubale saboda mawuyaci ne a gano yadda kungiyar IS ke jawo hankalin mabiyan ta.

XS
SM
MD
LG