Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce Zata Fice daga Kungiyar Raya Ilmi, Kimiyya da Al'adu, UNESCO


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Amurka ta ce za ta fice daga Kungiyar Raya Ilmi, Kimiyya da Ala’du ta Majalisar Dinkin Duniya wato – UNESCO, bayan da ta zargi kungiyar da nuna adawa da wariya ga Isra’ila.

A ranar 31 ga watan Disambar badi, ficewar Amurka daga kungiyar zata fara aiki, a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurkan.

Sa’oi kadan bayan wannan sanarwar da Amurka ta fitar, ita ma kasar ta Isra’ila ta ayyana cewa za ta fice daga kungiyar.

Tuni wata sanarwa da Ofishin firai ministan Isra’ila ya fitar, ta nuna an baiwa ma’aikatar harkokin wajen kasar umurnin fara shirye-shiryen ficewa daga kungiyar ta UNESCO tare da Amurka.

Firai ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya kwatanta matakin da shugaba Donald Trump ya dauka a matsayin na jarumta.

A wani martani da ta mayar, Kungiyar ta UNESCO, ta nuna takaicinta kan ficewar Amurka, wacce ta ce mamba ce da aka kafa kungiyar da ita.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta ce daukan wannan mataki ya zama dole tun bayan da kungiyar ta yanke shawarar cewa tsohon Birnin Hebron da kuma wasu muhimman kaburbura a matsayin wurare da ke yankin Falasdinawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG