An cilla wasu ‘yan sama jannatin Amurka biyu sama zuwa sararin subahana a jiya Asabar, a karon farko a wani kumbon wani kamfani mai zaman kansa, bayan kusan shekaru 10 da aka cilla wasu ‘yan sama jannati daga Amurka.
‘Yan sama jannati Doug Hurley da Bob Behnken sun doshi falaki da karfe 3:22pm akokon Gabashi, kamar yadda aka tsara, daga Tashar Kumbon Kennedy da ke Cape Canaveral, jahar Florida, a wata roka, wadda wani kamfani mai zaman kansa ya zana ya kuma gina. Ana kyautata zaton za su isa Tashar Kasa da Kasa a yau dinnan Lahadi.
Kamfanin na kumbo wanda ke California mai suna SpaceX, mallakin wani attajirin biloniya ne mai suna Elon Musk.
(Kafin a harba kumbon)
“Bari mu kunna wannan kendir din,” a cewar kwamanda Hurley a gabanin tashin kumbon, wanda wannan ita ce kalmar da Alan Shepard ya yi amfani da ita a kumbon Amurka na farko da ya cilla dan adam sama a 1961.
Shugaban Amurka Donald Trump da Mataimakin Shugaban kasa Mike Pence sun tafi Florida ta jirgin sama wajen cilla kumbon, wanda shi ne karo na biyu da su ka je wurin a wannan satin. Wasu ‘yan kallo sama da miliyan 3 sun taya shugabannin kallo ta yanar gizo, bisa ga kididdigar NASA, haka zalika wasu ‘yan kallon kuma da su ka
Facebook Forum