Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Dage Takunkumin Da Ta Sanyawa Kamfanin Jiragen Saman Qatar


Fasinjoji na shiga jirgin saman Qatar

Kamfanin jiragen saman Qatar da tashar jirgin saman kasa-da-kasa ta Hamad sun cika sabbin ka’idodin tsaro da Amurka ta gindaya.

Kamfanin jirgin saman Qatar ya ce fasinjojinsa yanzu za su iya daukar na’urar kwamputar ta tafi-da-gidanka da wasu na’urori masu amfani da lantarki cikin jiragen saman dake tafiyar kai tsaye zuwa Amurka.

A watan Maris ne Amurka ta hana shiga da kwamputar laptop da manyan na’urori masu amfani da lantarki wurin da pasinjoji ke zama, a jiragen dake zuwa Amurka daga tashoshin jirage 10 a gabas ta tsakiyar da arewacin Afrika saboda damuwar cewa ‘yan ta’adda za su iya boye bama-bamai a cikin na’urorin.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta cikin gida ta fada a makon da ya gabata cewa ya kamata kamfanonin jiragen su fara amfani da manyan na’urorin daukar hoton kaya na musamman wajen duba kayan da ake shiga da su wurin zaman fasinjoji, ko kuma su ci gaba da hana fasinjojin shiga da kayan latroni cikin jirgin.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG