Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi 'Yan Kasarta Kan Zuwa Kamaru


Ziyarar John Kerry Zuwan Najeriya.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta gargadi ‘yan kasar ta da su guji zuwa yankunan arewa mai nisa a kasar kamaru, saboda masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda da ke kai harin kunar bakin wake.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta kuma yi gargadin cewa irin dauki ko kuma tallafi da ofishin jakadancin Amurka ke bayarwa a wurare masu nesa takaitacce ne.

Har ila yau sanarwar ta kawar da sanarwa gargadi ta farko da aka fitar ranar 22 ga watan Disambar bara.

Kungiyar ta Boko Haram, ta kan kai hari akan ‘ya kasashen waje da masu yawon bude ido da shugabannin gwamnatoci a arewa mai nisa.

Akalla ‘yan kasashen wajen 37 aka yi garkuwa da su a wannan yankin tun daga shekarar 2013.

Kuma tun daga watan Yulin bara, kungiyar ta kai hare-haren kunar bakin wake 38 a yankin na arewa mai nisa ciki har da garin Maroua da ke Kamaru.

Ofishin jakadancin Amurka na ci gaba da dakatar da tafiye-tafiye a arewaci da arewa mai nisa da kuma gabashin Kamarun, tare da yankin Ngaoundere da ke Adamawa.

Sannan sanarwa ta kara da cewa akwai kuma barazanar fashin jiragen ruwa a yankin mishigin tekun Guinea a sashin Bakassi.

“Ya kamata Amurkawa su yi hattara wajen tafiye-tafiye tsakanin mil 60, wato kilomita 100 a tsakanin jihar Adamawa da ke Najeriya da yankin Adamawan Kamaru.” Sanarawar ta ce.

Dama dai akwai sakon gargadi ga Amurkawa da su guji wasu yankuna a Najeriya da Chadi da kuma Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG