Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta hallaka shugaban ISIS da kwamandojinsa a Afghanistan


Shugabannin ISIS a Afghanistan da suka halaka
Shugabannin ISIS a Afghanistan da suka halaka

Wani harin da jirgin Amurka mara matuki ya kai ya hallaka shugaban ISIS na Afghanistan tare da kwamandojinsa tara

Wani harin jirgin saman yaki da babu matuki da Amurka ta kai, ya kashe shugaban kungiyar ISIS a Afghanistan Abdu Saad Erthabi da kwamadojinsa guda tara.

Harin na makami mai linzami an kai ne a cikin dare a gundumar Khogyan a lardin Nangahar dake fama da rikici, inda kungiyar da ake cewa ISK-P take da hedikwatar ta.

Mai magana da yawun gwamnatin lardin Attaullah Khogyan ya fadawa Muryar Amurka cewa harin ya kuma lalata sansanonin kungiyar.

Ahalinda ake ciki kuma shugaban kasar Ashraf Ghani ya ki ya amince da ajiye aiki da manyan jami’an tsaron kasar ciki harda da ministan tsaro,ministan harkokin cikin gida,babban jami’in leken asiri, sun mika takardun barin aiki ranar Asabar.

Sun yi hakan ne jim kadan bayan da mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro ya mika tasa wasikar ajiye aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG