Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Harbo Wani Jirgin Yaki Maramatuki Na Iran A Syria.


Jiragen Yakin Amurka biyu samfurin F-15E Strike Eagles fly.
Jiragen Yakin Amurka biyu samfurin F-15E Strike Eagles fly.

Jami'ai a Amurka sun shaidawa Muryar Amurka cewar suna dab da tabbatar da ko rundunar juyin juya hali ta kasar Iran ce ta sarafa jirgin.

Jami'ai a Amurka sun shaidawa Muryar Amurka cewar suna dab da tabbatar da ko rundunar juyin juya hali ta kasar Iran ce ta sarafa jirgin da bashi da matuki kirar Iran da jirgin saman yakin Amurka ya harbo da safiyar jiya Talata.

Wasu majiyoyi a Amurka da suka zanta da Muryar Amurka da basu yarda da a bayyanasu ba, sun ce dogarawan Juyin juya halin na Iran sune suka sarafa wannan jirgi mara matuki daga wani sansanita dake cikin Syria. Sansanin ya na kusa da Hama a cewar wani jami'i.

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka da ake cewa Pentagon Navy Capt. Jeff Davis yace wani jirgin yakin Amurka sanfurin F-15E ko kuma Strike Eagle, ya harbo jirgi mara amfani da matuki kirar Iran samfurin Shaded 129 da misalin karfe 12 da rabi na rana agogon can, yayin da ya doshi sansanin rundunar kawance a kusa da al-Tanf, inda Amurka ke horar da sojojin yankin da suke yaki da IS.

Davis yace an gano wannan jirgin da babu matuki da aka lalata a jiya Talata a kusa da inda aka taba harbe wani jirgin na Iran da bai da matuki a ranar takwas ga wannan watan Yuni.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG