Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kare Takunkumin Da Ta Kakabawa Iran


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo

Biyo bayan karar da Iran ta kai Amurka a kotun duniya, Amurkan ta kare matakan kakabawa Iran takunkumi da ta dauka

Amurka ta kare matakin da ta dauka na sake kakaba takunkumi akan Iran, matakin da ta ce ta dauka bisa doka, domin ta tabbatar da tsaron kasarta, tana mai cewa Tehran ba za ta iya kalubalantar matakin ba a babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya.

Mai ba da shawara a sashen shari’a a ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Jennifer Newstead, ta yi kira ga alkalan kotun kasa da kasa, da su yi watsi da bukatar gaggawa da Tehrna ta gabatar, ta a dakatar da takunkumin da shugaba Donald Trump ya sake kakabawa Iran a watan Mayu.

Sai dai ta nanata cewa, takunkumin ba su shafi ayyukan jin-kai a Iran din ba.

Akwai dai yiwuwar sai an kwashe har makonni kafin kotun ta yanke shawara, kan wannan bukata ta gaggawa da Iran din ta gabatar a gaban kotun.

Kotun wacce take warware rikici tsakanin kasashe,babu daukaka kara, saura dame, ko Amurka zata mutunta umarnin kotun na janyen takunkumin, shine abun jira a gani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG