Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Karfafa Matasa Ma'abuta Kafar blog a Nijar


Kungiyar Matasan Nijar

A wani mataki na dada karkatar da tunanin matasan Janhuriyar Nijar daga miyagun ayyuka, Ofishin Jakadancin Amurka da hadin gwiwar wasu kungiyoyin kasar ta Nijar, ta karrama mafiya kwarewa a gasar amfani da kafar blog.

Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijar, da hadin gwiwar Majalisar Matasan kasar da Kungiyar Mata Ma’ikatan Yada Labarai, sun karrama wasu matasan da suka lashe gasar lakantar hikimomin amfani da kafar sada zumunta ta blog da nufin kara masu kwarin gwiwa a wannan aiki na fafitikar kare hakkin jama’a.

Gomman matasa daga sassa daban daban na kasar Nijar ne suka fafata a wannan gasa da ta kasance wata damar tankade da rairaya domin tantance wadanda suka fi lakantar fasahohin amfani da kafar sada zumunta ta Blog bayan samun horo akan dabarun yada labarai a irin wadanan kafafe. Jami’in hulda da ‘yan jarida a ofishin jakadancin Amurka a Nijar Idi Baraou ya yi min Karin bayani da dalilin hakan shi ne a kwadaita ma matasa shiga harkokin kwarai a maimakon mayar da hankalinsu kan abubuwa marasa kyau.

Twitter logo
Twitter logo

Matasan da suka yi nasara a wannan gasa sun sami kyaututtukan da suka hada da na’urori na daukar hoto da komfuta da dai sauransu.

Majalisar Matasan Nijar (CNJ) da Kungiyar Mata Ma’aikatan Yada Labarai (APAC Niger) da suka yi ruwa da tsaki wajen ganin gwamnatin Amurka ta dauki nauyin bai wa matasa horo akan hikimomin amfani da kafafen sada zumunta na daukar abin tamkar wani matakin kare wannan rukuni na al’umma, inji shugaban majalisar ta CNJ, Alio Oumarou.

Bukin karrama wadanan matasa ya yi dai dai da lokacin da darektar cibiyar raya al’adun kasar Amurka Mme Cyntia Fabi ke shirin komawa gida, bayan kammala aikin da ta shafe shekaru 3 ta na gudanarwa a nan Nijar. Gudunmowar da ta bayar wajen karfafa dangantakar Amurka da jama’ar wannan kasa ya sa majalisar CNJ da Kungiyar APAC Niger karrama ta da lambobin yabo ba’idin wasu kyaututtuka na musamman.

Ga Suleiman Barma da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00Facebook Forum

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG