Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sakawa Venezuela Takunkumin Karya Tattalin Arziki


Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana manufarsa na sakawa kasar Venezuela Takunkumin da zai dakatar da wasu kaddarorin da kamfanin PDVSA ke da su a Amurka.

Gwamnatin Shugaba Trump ta Amurka na yunkurin saka ta kunkumi akan kamfanonin man fetur din kasar Venezuela, inda take cewa tana son ta yin haka ne don adana wa mutanen Venezuela kaddarorin kasarsu.

A jiya ne Mai bada shawara ga harkokin tsaron na Amurka, John Bolton yake cewa yan kasar Venezuela sun dade suna shan wahala dalilin manufofin gwamnatin shugaba Nicolas Maduro.

Takunkumi dai zai takatar da duk wasu kaddarorin da kamfanin PDVSA ke dasu a Amurka da kuma tabbatar da an hana yan kasar yin kasuwanci da kamfanin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG