Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kashe Mayakan Al-Shabab 13 a Somalia


Sojojin Amurka
Sojojin Amurka

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta fada a jiya Laraba cewa wani hari ta sama da aka kai a Somalia a jajibirin Krismeti ya kashe mayakan al-Shabab 13. Rundunar hadin gwiwan Amurka da Afrika tace gwamnatin Somalia ta timaka wurin shirya kai wannan farmakin a arewa maso yammacin Kismayo.

Rundunar tace, farmakin ya auna yan ta’addan ne yayin da suke shirin kaddamar da wani hari a kan sasanin sojan na Amurka, amma sai aka yi sa’a, sojojin wata kasar da Amurka ke kwance da ita suka ruguza aniyarsu da farmaki daga jirgi mara matuki kuma ya kashe akalla mutane 13, inji Kwamanda rundunar Somalia a yankin, a hirar da yayi da Murya Amurka.


Amurka ta kai farmaki ta sama a kan al-Shabab sau 30 a cikin wannan shekarar, ciki har da amfani da jirgi mara matuki da ya auna sansanin horar da mayakan ‘yan ta’addar a wata da ya gabata kuma ya kashe dari daga cikinsu.


Wani babban hafsan sojin Somalia ya fada a jiya Laraba cewa sama da mayakan l-Shabab guda ashirin ciki har da kananan kwamandoji biyu, sun mika kansu ga rundunar Somalia a cikin makwanni biyu da suka wuce.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG