Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta kashe wani jigon ISIS a Iraqi yankin kurdawa


Ashton Carter, Sakataren Tsaron Amurka

A Iraqi, majalisar tsaro ta yankin kurdawa, tace wani hari na musamman karkashin jagorancin Amurka ya kashe wani jigo a kungiyar ISIS.

Jami'an tsaro a yankin na kurdawa suka ce harin da jiragen yaki da aka kai ranar 16 ga watan nan ya kashe wani da ake kira Khaled Afer, mai inkiyar Abu Sarya. Shine yake baiwa kungiyar shawara kan harkokin tsaro a Mosul, kuma na hanun daman kakakin kungiyar, Abu Mohammed al-Adnani ne.

Harin da aka kai ranar Asabar an kaishi ne a wurin da ake kira Sahel al Aysa, kusa da asibitin Salam.

Ahalinda ake ciki kuma, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, jiya Talata ya gana da takwaran aikinsa na Iran Mohammed Javad Zarif, da zummar ganin Iran ta sami sassauci daga takunkumin da hukumomin kasa da kasa suka aza mata da aka yi mata alkawarin janyeshi karkashin yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla da kasar cikin watan Janairun bana.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG