Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin warware rikicin kasar Syria ya samu koma baya


Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura dake shiga tsakanin gwamnatin Syria da masu hamayya
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura dake shiga tsakanin gwamnatin Syria da masu hamayya

An fuskanci koma baya a yunkurin warware rikicin da ake yi a Syria ta fuskar Syria, bayan da babbar kungiyar 'yan hamayya a shawarwarin sulhun da MDD take shiga tsakaninta da gwamnatin Syria ta janye, ta kuma nemi taimakon manyan kasashen duniya da suke mara musu baya su taimaka mata.

Babbar kungiyar 'yan hmayyan ta zargi gwamnatin Syria da laifin karin fadace fadace da suke aukuwa tun bayan da asassan biyu suka sanya hanu kan yarjejeniyar tsagaita wuta.

A wani taro da manema labarai jiya Talata a birnin Geneva, shugaban 'yan hamayya Riyad Hijab, yayi kira ga kasashen duniya a zaman magoya bayan Syria su sa baki.

Ahalinda ake ciki, 'yan gwagwarmaya a Syria sun ce wasu farmaki dajiragen yaki da aka kai kan garurwa biyu dake hanun 'yan hamayya a arewa maso yammacin Syria, ya kashe mutane 44.

Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Bil'Adama a Syria, tace farmaki da aka kai kasuwar kayan gwari, a garin da ake kira Maarat-al-Numan, jiya Talata ya kashe kimanin mutane 40. Kungiyar mai zaman kanta tace wani harin kuma da aka kai kan wani gari mai suna Kafranbel a lardin Idlib ya kashe akalla mutane hudu. An san duka yankunansuna zaman tungayen 'yan hamayya ne.

XS
SM
MD
LG