Ba tare da ba da cikakken bayani akan abinda ya kai ga ayyana samun nasara akan mayakan kungiyar ISIS dake Syria ba, Fadar White House ta kare ikirarin da kuma matakin fara dawo da sojojin Amurka da ke kasar ta Syria da yaki ya daidaita gida.
Wannan sanarwar, da ta ba wasu jami’an tsaro, da jami’an diflomasiyya da ma ‘yan majalisar dokokin kasar mamaki, a shafin twitter Shugaban Amurka Donald Trump suka fara ganinta jiya Laraba da safe.
“Mun sami nasarar magance ‘yan ISIS a Syria,” abinda shugaban ya rubuta kenan a shafinsa na twitter.
Wannan sanarwar ta kai ga jefa alamar tambayoyin da suka tilastawa jami’an fadar white house da na ma’aikatar tsaron Pentagon, yin bayani akan sakon na shugaban.
“Amurka ta fara maido da dakarunta, gida a yayinda kasar ta shiga wani sabon babi na yaki da ‘yan ta’adda,” a cewar sakatariyar yada labaran fadar white house Sarah Sanders, ta kara da cewa samun nasara akan ‘yan ISIS ba ya na nufin yakin da sojojin hadaka ke yi a Syria ya kare bane.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum