Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Nemi a Daga Zaben Burundi


Shugaba Barack Obama.

Amurka ta bukaci kasar Burundi da ta jinkirta gudanar da zaben kasar da aka shirya yi, bayan da aka kwashe makwanni ana fama da rikicin siyasa.

A jiya Juma’a kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Jeff Rathke, ya ce yanayin da kasar ke ciki ba zai ba da damar a gudanar da zabe mai inganci ba.

Ya kuma ce Amurka ta shiga damuwa matuka, bayan wasu hare-haren gurneti da aka kai, da rikicin da tsagerun ke haifarwa, da tsaurara matakan hana zanga zangar lumana da walwalar ‘yan jarida, duk suna yin hanun riga a kokarin da ake yi na shawo kan rikicin.

A harin gurneti da aka kai a kofar wani banki da ke Bujumbura, wani dan karamin yaro ya samu rauni, sannan wasu mutane biyu sun halaka a wasu hare-hare na daban da aka kai a ‘yan kwanakin nan.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi ‘yan sandan kasar da wuce-gona-da-iri a kokarin da suke yi na tarwatsa masu zanga zanga, wadadan ke adawa da yunkurin da Shugaba Pierre Nkurunziza ke yi na neman tazarce.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG