Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Kira Akai Zuciya Nesa Kan Rikicin Isra'ia Da Yankin Falasdinu


Masu zanga zanga a yankin Falasdinu, baya da Isra'ila ta harba musu borkonon tsohuwa.

Shugaba Obama ne yayi wannan kira a wani taro da manema labarai

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana damuwa kan barkewar tarzoma a birnin kudus, inda yayi kira ga shugabanin yanki su "hana" amfani ko furta kalamai da zasu ruruta wutar tarzoma, ko fusatar da jama'a, ko haifar da rashin fahimtar juna."

"kuma bana jin sai mun jira an cimma daidaito kan dukkan batutuwa da suke akwai tsakanin Isra'ila da Falasdinawa kamin mu kashe wannan wutar",inji shugaban na Amurka jiya jumma.

Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurka zai gana da PM Isra'ila Benjamin Netanyahu makon gobe watakil a Jamus yayinda Me. Netanyahu yake ziyarar aiki a can.

Ahalin yanzu kuma, idan ka tambayi masu nazari kan al'amuran yau da kullum a yankin Falasindu da Isra'ila kan musabbabin tashe tashen hankula da suke aukuwa, zaka sami bayanai ko dalilai masu karo da juna.

Wata lauya mai kare 'yancin Bil'Adama Ba-Falasdiniya, Diana Buttu, tace kona gidan wani BaFalsdine a yammacin kogin Jordan a karshen watan Yuli, har dansu dan shekara daya da rabi da haifuwa ya mutu, kamin iyayensa wadanda suma suka jikkata sosai a harin suka bi dan nasu daga bisani, a zaman dalilin wannan rikici.

Amma wani mai fashin baki a Isra'ila wanda yake da majiyoyi a a majalisar dokokin kasar, yace kashe wani bayahude da matarsa a gaban 'yayansu hudu cikin wannan wata, da kuma batunda yahudawa suke cewa ina 'yancin addinin idan ba za'a kyale su suyi ibada a wuri mafi daraja na uku ga musulmi, wanda shine wuri na farko a daraja ga yahudawa?

Bayan da Isra'ila ta kama birnin kudus a yakin da tayi da kasashen Larabawa 1967, Isra'ila ta yarda zata mutunta hana yahudawa na yin iabda a wurin mataki da ake amfani da shi fiyeda shekaru dubu daya lokacinda masallacin yake karkashin daular Ottoman.

XS
SM
MD
LG